Messi Yana Fushi Da Shugaban Barcelona Akan Rashin…

139

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wato Leonel Messi yana fushi da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wato Josep Bortameu akan gazawarsa ta kasa dawo da Neymar Barcelona.

Inda su kansu kungiyar kwallon kafan ta PSG suka baiwa Barcelona dama idan har suna so to su cakemusu kudi subasu Neymar kokuma su basu wasu ‘yan wasa su hadamusu da kudi amma sun kasa.

Shine Leonel Messi yake ganin laifin shugaban kungiyar kwallon kafan ta Barcelona ne tunda yaki yamai da hankali kuma ya saki kudi domin dawo dashi Kungiyar.

Amma idan za a iya tunawa Barcelona sun zubawa Neymar kudi kuma ahaka PSG suka saya shine yanzu Barcelona suka sake komawa neman Neymar shine suma suka zabgamusu kudi.

Abin da Messi yake fargaba shine matukar Barcelona suka gaza sayen Neymar to babu makawa za a iya tsintarsa a babbar abokiyar hamayyar Barcelona wato Real Madrid.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan