Gwamnatin tarayyar ƙasar nan da gamayyar ƙungiyar ‘yan kwadago za su zauna domin ɗaukar matakin ƙarshe akan maganar mafi ƙarancin albashin ma’aikata
Tun da farko dai Jaridar The Nation ce ta ruwaito cewa ana sa ran za’a cimma matsaya guda wadda kuma za ta kasance ta ƙarshe bayan wannan ganawar.
Ministan ƙwadago Sanata Chris Ngige ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa maganar mafi karancin albashi ita ce akan gaba a cikin ayyukan da zai soma yi da zarar ya shiga ofis.
Har yanzu dai an kasa cimma matsaya guda wadda za ta bada damar soma biyan sabon mafi ƙarancin albashi da shugaban ƙasa ya rattabawa hannu tun 18 ga watan Afrilu.
Turawa Abokai