Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Fara Shirin Karɓar Bashin Da Ta Ke Bin Jihohin Ƙasar Nan

138

Gwamnatin tarayya ta fara wani shirin tattaro tulin kuɗaɗen lamunin da ta arawa jihohin kasar nan guda 34 ban da jihar Lagos wadanda yawansu ya kai Naira biliyan 614, wannan matakin yana zuwa ne bayan shugaban rantsar da ministocinsa.
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmad tuni ta jagoranci taron kolin tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, in da ya amince da kafa wata tawaga daga kungiyar gwamnonin kasar nan wadanda za su gana da babban bankin domin fara daukar matakin dawo da kudaden.
Rahotanni sun bayyana cewa kowacce jiha cikin jihohin 35 ta karɓi kuɗin da yawansa ya kai Naira biliyan 17 da rabi in banda jihar Lagos.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan