Ra’ayi: Darasi Tun A Duniya (1)

129

Na kasa gano lokacin da Al’ummata zata gyaru, a har kullum muane basa ganin matsala sai ta zo kansu…

Abu na farkoda ya ja hankalina har nayi wannan batu shi ne: Mafiya yawan masu karanta rubuce-rubuce na sun san ina kan dokar daina rubutu har tsawon wani lokaci saboda nayi rubutu a kan FYAƊE ba ni da matsala a lokacin da nayi rubutun littafina mai suna Budurwa a ƙasar Hausa da kuma Banbancin Tarbiyya da Ilimi Amma kwatsam sai wata Tarzoma ta ɓarke saboda nayi rubutu a kan FYAƊE.

Sanin kowane babu cin mutunci da cin zarafin da yafi FYAƊE a wajen ƴaƴa mata, FYAƊE masifa ne, kuma Bala’i ne, FYAƊE kaɗai abinda yake faruwa ga mace ta kasa mantawa har ta koma ga mahalicci, Mata kan manta ciwon laulayin ciki da na naƙuda da mutuwar Uwa ko Uba amma basa manta lokaci, Yanayi, ko kuma Wurin da aka yi musu FYAƊE

FYAƊE ne Abu ɗaya da ya kansa mace ta ji ta ba dai-dai ba ko kuma ta ji a ranta cewa ita bata cika ba ko kuma tana da wani naƙasu ta wani bangare.

Ƴan Mata da dama kanyi harkokin bariki ko bin mazaje ba tare da jin sun rasa wata daraja ko kima a idon mutane ba, amma da zarar ance an yiwa mace FYAƊE sai ya zame mata wani mummunan shafi a cikin Littafin qaddararta, wanda ba ya wucewa.

Irin wannan Zalunci da Cin zarafin ne ya sanya ra’ayi na ya karkata kan Rubutu game da wannan matsala. Amma an Hana ni sakin yawancin rubutun saboda Ina karkashin ikon masu iko da ni.

Amma nayi Addua a wancan lokaci nace ” InshaAllah Wanda ya assasa hanani sakin rubutun Nan sai ya ji ɓacin ran da iyayen da aka yiwa ƴaƴansu FYAƊE su ke ji.

Na samu Kira a yau daga wannan bawan Allah Kuma ya Tabbatar min an yiwa jikarsa yar shekaru 12 FYAƊE na ji Masa takaici Kuma na jiwa yarinyar ciwon abinda ya sameta.

Mutumin yayi Nadama akan abinda yayi min ya kuma ce da ace bai sa an hanani ba da yanzu ba’asan adadin ƴan Matan da Rubutu na zai kuɓutar ba.

Saƙo na anan shi ne: A kullum ka zamto Mai jin ciwon abinda ya samu waninka domin baka san irin abinda zai same ka ba ta haka ne zamu gina Al’umma ta gari…..

Daga ƙarshe Ina muku Albishir Insha Allah farkon shekara Mai zuwa zan koma harkar Rubuce-Rubuce na kamar a baya…..

Daga Zunnura Ishaq Jibriel

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan