Home / Labarai / Zamu Kaiwa Shugaba Buhari Hari A Ƙasar Japan – Nnmadi Kanu

Zamu Kaiwa Shugaba Buhari Hari A Ƙasar Japan – Nnmadi Kanu

Jagoran kungiyar ‘yan kabilar Ibo masu neman kafa kasar Biyafara Nnamdi Kanu, ya umarci membobin kungiyar da ke zaune a ƙasar Japan a kan su wulakanta tare da kama Shugaba Muhammad Buhari a lokacin da ya isa kasar domin halartar Taron Duniya na Bakwai a Tokyo.

Nnamdi Kanu ya fadi haka ne a ranar Jumu’a inda ya nuna membobin kungiyar su tabbatar sun tsara yadda za su kama Buhari. Ya ce sun shirya wa duk wata shari’a da za a yi daga bisani.

Wannan magana ta jagoran ‘yan Biyafaran ta fito ne jim kadan bayan mai ba shugaban kasa shawara na musamman a harkar kafafen yada labarai, Mista Femi Adesina, ya sanar wa ‘yan Nijeriya cewa a ranar Lahadi Shugaba Buhari zai bar Nijeriya don zuwa Japan halartar Taron Duniya na Bakwai a Tokyo, wanda za a yi a birnin Yokohama daga 28-30 ga Agusta, 2019.

Nnamdi Kanu ya ce dalilin wannan shiri nasu domin su sanya Shugaba Buhari ya amsa tambayoyin da suke da su a kan kashe-kashen da suke zargin ya yi wa mutane daga 2015 zuwa 2019 na zangon mulkinsa na farko.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *