Gwamna El-Rufai Zai Fara Biyan Ma’aikatan Kaduna Sabon Albashi Na Naira 30,000

70

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000 daga ranar 1 ga watan Satumbar shekarar 2019.
Gwamnatin jihar ta yanke shawarar fara biyan sabon albashin ne a karshen zaman majalisar zartarwar jihar daya gudana a yau Litinin karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe.
Tun da farko dai gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne domin inganta walwala da jin daɗin ma’aikatan jihar, inda tace hakan ne yasa tun a shekarar 2018 gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai duba yiwuwar karawa ma’aikata albashi.
“Muna duba karfin iya biyan albashin da kuma karfin iya cigaba da biyan albashin ba tare da yankewa ba, mun duba yadda jihar Kaduna take tattara Kuɗaɗen shiga da kuma kuɗin da take samu daga asusun gwamnatin tarayya.
“Aiwatar da sabon ƙarancin albashi na ƙasa na naira 30,000 zai ƙara adadin kuɗaɗen da gwamnatin jihar Kaduna ke kashewa wajen biyan albashi da kashi 33, daga naira biliyan 2.82 zuwa naira biliyan 3.79, wannan kari na kusan naira biliyan 1 na nufin albashi da fansho zai kwashi kaso mai tsoka na kudaden jihar Kaduna.
“Domin haka biyan wadannan makudan kudade, tare da kokarin samar da ababen cigaba da more rayuwa na nufin karin nauyi akan gwamnati na kara fadada hanyoyin neman kudaden shigarta.”
Aiwatar da wannan sabon tsarin karancin albashi zai kara adadin albashin karamin ma’aikaci a jihar Kaduna dake karbar mafi karancin albashi da kashi 67, yayin da albashin matsakaitan ma’aikata daga mataki na 10-14 zai haura da kashi 60.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan