Ya Kamata A Fara Amfani Da Harshen Hausa A Makarantunmu – Farfesa Aliyu Bunza

298

Fitaccen masanin harshen Hausa na jami’ar Usman Ɗanfodio da ke Sokoto Farfesa Aliyu Bunza ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a dinga amfani da harshen Hausa a dukkanin makarantun da su ke faɗin ƙasar nan, musamman a makarnatun da su ke yankin arewacin ƙasar nan.


Farfesan ya bayyana haka ne a gurin taron Hausa na duniya wanda ƙungiyar Hausa ta Ƙasa ta shirya tare da haɗin gwiwar jami’ar Bayero da ke nan Kano.


“Lokaci ya yi da ya kamata a ce ana koyar da ɗalibai a dukkanin fannoni da harahen Hausa. Idan da za’a ce za’a koyar da ɗaliban da su ke nazarin aikin Likita ko injiniya ko kimiyyar haɗa magunguna, to babu shakka sai an zo daga ko ina a faɗin a duniya neman ƙwararun da su ka samu ilimi da harshen Hausa”


Farfesa Aliyu Bunza ya ƙara da cewa irin asarar da Ingilishi ta kawo mana, yafi na yaƙin basasa. Domin karamin misali idan ka je kotunan shari’a za ka tarar tun daga kan alkali har zuwa kan wanda ake tuhuma da laifi sun nakaltar yaren Hausa fiye da kowanne yare.


Taron dai ya samu halartar manyan baƙi daga sassa na ciki da wajen ƙasar nan, waɗanda su ka haɗa da Dalibai daga jami’ar birnin Bejin daga ƙasar China.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan