Yadda Aka Soke Sakamakon Zaɓen Gama- Farfesa Abdussalam

185

Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen Ƙaramar Hukumar Nasarawa a yayin Zaɓen Gwamna na 9 ga watan Maris a Jihar Kano, Farfesa Ibrahim Khalil Abdussalam, ya faɗa wa Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna dake zamanta a Kano cewa an soke zaɓen Gama ne a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Jihar Kano.

Farfesa Abdussalam, wanda shaida ne da kotun ta ba umarni a rubuce da ya zo ya bada shaida, ya kuma faɗa wa Kotun cewa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓen ne ya gano wasu kurakurai a sakamakon zaɓen na Gama.

Ya ce bisa wannan dalili ne ya umarci Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen na Gama da ya koma ya gyara kurakuran.

Mista Abdussalam ya ce a sakamakon waɗannan kurakurai, wakilan jam’iyyu suka amince a tsakaninsu cewa a soke sakamakon domin kuwa ba za su amince da shi ba.

“Dokta Umar Tanko Yakasai, wanda shi ne wakilin tattara sakamako na PDP, ya karɓi rigimar, ya kuma rubuta rubutacciyar yarjejeniyar a madadin wakilan jam’iyyun”, in ji shi.

Shaidar ya kuma faɗa wa kotun cewa bayan nan ne sai Dokta Yakasai ya dawo ya ce ya tuntuɓi wani lauya, wanda ya ba shi shawara da kada ya karɓi soke sakamakon zaɓen, yana mai cewa bai dace ba.

Ya ce daga nan ne sai Mista Yakasai ya ɗauki hoton rubutacciyar yarjejeniyar, sannan ya yaga ta.

Mista Abdussalam ya ce da misalin ƙarfe 1 na daren 11 ga Maris, yayinda ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Ƙaramar Hukumar, sai aka samu hayaniya a wajen, aka ture shi can gefe, inda ya kusa faɗuwa, sannan aka ɗauke sakamakon daga kan teburinsa.

Ya kara da cewa dole ya ruga da gudu ya nemi mafaka.

A lokacin binciken ƙwaƙwaf, lauyan PDP, Eyitayo Fatogun, ya tambayi shaidar ko yarjejeniyar da aka samu tsakanin wakilan jam’iyyun ita ce dalilin soke sakamakon, inda ya ce a’a.

Mista Fatogun ya kuma tambayi Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen ko ya samu rahoton tashin hankali daga jami’an sanar da sakamakon zaɓe a mazaɓun yankin, ya kuma tambaye shi ko an soke wasu daga cikin sakamakon zaɓen a tashoshin zaɓen, inda ya ce a’a, yana mai jaddada cewa an fa soke sakamakon zaɓen ne a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Jiha.

A gefe ɗaya kuma, wanda ake ƙara na biyu, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kammala gabatar da shaidunsa bayan da ya gabatar da shaidu huɗu, waɗanda suka haɗa da Darakta Janar na Kamfe ɗinsa, Alhaji Nasiru Aliko Ƙoki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan