Fitaccen ma’aikacin rediyon nan kuma tsohon shugaban gidajen tarayya Kaduna da kuma jihar Kano wato Alh. Halilu Ahmed Getso ya bayyana wasu abubuwa guda uku da su ke cutar da aikin rediyo a wannan zamnin.
Halilu Getso ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilan gidan jaridar AMINIYA a gonarsa da ke kauyen ƴar bagaruwa a ƙaramar hukumar Gwarzo.
“Babu abin da yake cutar da aikin rediyo a yau, illa abubuwa guda uku. Na farko yaran da ake ɗauka suna aikin rediyo hori suka yi ba su gasu ba. Idan gasawa ake yi, ba su gasu ba. Idan dafa wa ake yi, danyu ne ba su dahu ba. Idan nuna ake a jikin reshe, to su ba su nuna ba aka tsinko su. Yaro ne bai san komai ba, bai iya komai ba, sakandire ya yi, ko ya yi Gired-tu ko ya yi Difloma a aikin jarida, sai ya fito yana hura hanci. Kana daukar sa kana saka shi a gidan rediyo, abu na farko da zai fara so shi ne a ji sunansa. Yau ga wane a gidan rediyo yana magana, kun ji ma yanzu ya fada mana sunansa. Tallar suna da son iyawa da gwadare. A jimla daya sai yaro ya hada karin magana biyu ko uku amma duk ba su da alaka da juna. Sai a fadi karin magana a gabar da ba ta dace a inda bai dace ba, kuma ba a daidai ba. Sannan kuma akwai girman kai na kin yin tambaya”
“Da Hausar da komai ma bai ishe su ba. Yanzu da yawa yaran da suke aikin Rediyo a nan kasar, wadanda ake dauka, ko abin da ake kira ilimin sanin kasa, ba su sani ba. Muna nan yanzu da kai yaro zai nuna inda dambatta take, nan zai nuna (Kudu). Ka san kuwa ba nan wajen take ba ko? To idan ana magana sai ka ji ya ce “wata rana na je nan dambatta.” Kai daga ganin wannan ka san bai san dambatta ba, bai san inda take ba. Ai da kunya kana Bakano, kana zaune a Gwarzo, za ka nuna inda dambatta take, kuma ka nuna Kudu. To irin wannan girman kan ga shi ba karatu, ko na jaridar nan ma da ake bugawa yau da kullum, ta Hausa da ta Turanci, yaran nan ba sa kokarin karantawa. Kuma akwai ilimi mai yawa a ciki. Duk inda ka kai da sanin wani abu, wallahi idan kai ma’abucin karatun jaridu ne da littatafai yau da kullum sai ka tarar da abin da ba ka sani ba, ko a jaddada maka sanin abin da ka sani. Yaran yanzu babu ruwansu ba sa yin wannan”
“Sannan na uku hakuri. Wanda duk ba shi da hakuri a al’amarin duniya to karshenta za ka ga rabonsa ba shi da yawa. Suna da ci da zuci yaran yanzu. Sauri suke gaf gaf gaf. Jiya-jiyan nan yaro yana makaranta, bayan ya gama ya fito da wata hudu, jihadin da yake yi shi ne a gan shi da mota. Bai tsaya ma ya koyi aikin ya yi shi yadda ya kamata ba, amma kulle-kullen da yake yi, shi dai ya yi mota dai. A gan shi dai a ce “yau wane shekararsa daya da kama aiki, ka ga har ya yi mota.”
A ƙarshe ya bayyana cewa waɗannan su ne abubuwan da su ke cutar da kowane aiki.
“Kamar yadda na fada maka. Ba aikin rediyo ba ko aikin kwashe kashe, wallahi sai an saka wata godiya da wadatar zuci. A rika ba zuciya hakuri ana taka mata birki. Can kake so ka je? Tafi a hankali, ka daina garaje. Idan Allah Ya yarda za ka je”
Abubuwa Uku Ne Su Ke Cutar Da Aikin Rediyo A Wannan Zamnin – Halilu Ahmed Getso
Turawa Abokai