Folconest Zasu Kara Wasan Karshe da Kasar Cameroon

162

Kungiyar kwallon kafan mata ta Najeriya ta ‘yan kasa da shekara 20 wato Folconest zata fafata wasan karshe da kungiyar kwallon kafan mata ta kasar Cameroon acigaba da wasannin motsa jiki da akeyi a kasar Morroco.

Inda za a fafata wasan karshen a ranar Alhamis 29 ga watan Ogusta nan na 2019.

A wasan kusa dana karshe kasar Cameroon ta lallasa kasar Morocco daci 3 da 1.

Ita kuwa kasar Najeriya ta casa kasar Algeria daci 3 da nema.

Tun a rukuni Najeriya da Cameroon sun hadu inda suka tashi kowacce Kungiya nada ci 1.

Zasu kara wannan wasa na karshe da misalin karfe 5:00 agogon Najeriya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan