Majalisar Dokokin Jihar Legas ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda gwamnatin tsohon Gwamna Akinwunmi Ambode ya siyi mitocin bas-bas 820 a jihar.
A makon da ya gabata, jami’an Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC sun binciki gudajen tsohon gwamnan dake Ikoyi da Epe a wani ɓangare na ci gaba da binciken cin hanci da ake yi masa.
A makonni uku da suka gabata, wani alƙalin Kotun Tarayya ya kulle wani asusun bankuna masu ɗauke da Biliyan 9.9 da ake zargin na tsohon gwamnan ne.
Mista Ambode ya musanta cewa yana da alaƙa da asusun bankunan.
Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataMajalisar Dokokin Legas Ta Fara Binciken Tsohon Gwamna Ambode Bisa Badaƙalar Siyan Bas-bas […]