NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2019

196

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Ƙasa, NECO, ta saki saki sakamakon Jarrabawar Kammala Babbar Sakandire ta June/July ta 2019 wato SSCE.

Muƙaddashin Magatakardar Hukumar, Abubakar Gana ya sanar da haka a Hedikwatar Hukumar dake Minna, a Jihar Naija ranar Talatar nan.

Ya ce kaso 71 cikin ɗari na ɗalibai sun samu ‘credits’a Turanci da Lissafi.

Ana shirya Jarrabawar SSCE ne ga ɗaliban dake shekarar ƙarshe (SSSIII) a babbar sakandire.

NECO tana yi wa ɗalibai jarrabawar ne a darussa 76, da suka haɗa da darussan suka zama wajibi, darussan nazarin ɗan Adam, da darussan kasuwanci ko koyon sana’a.

Dole ɗalibai su yi darussa huɗu daga cikin darussan da suka zama dole, sannan darussa uku zuwa huɗu daga abinda suke nazarta, da darasi ɗaya na zaɓi wanda ba ya cikin abinda suke nazarta, matuƙar dai ba su wuce darussa tara ba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan