Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta aikewa da fitaccen mawaƙin nan Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) sammaci. Takardar sammacin ta buƙaci mawaki Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) [Dan Amanar Bicci] da ya mika kansa ga ofishin hukumar a ranar Litinin, 02 ga watan Satumba, 2019, akan wani binciken laifi da hukumar take yi.
Takardar mai ɗauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ƴan sanda DCP Paul ɓangaren binciken laifukan ta’addanci, ta buklƙaci mawaƙin ya fara miƙa kansa ga jami’in ofishin da ke kula da harkokin binciken laifuka akan harkokin siyasa.
Idan za’a iya tunawa dai a watan da wuce ne Mai Martaba Sarkin Bichi, Alh. Aminu Ado Bayero ya naɗa Aminu Ala sarautar Ɗan Amanar Bichi.
Kawo yanzu dai babu wani martani da aka ji daga bakin mawakin
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Tana Neman Alan Waƙa
Turawa Abokai