Shugaba Buhari Ya Manta Da Jiharsa Ta Katsina – Mubarak Ibrahim

208

Baba Buhari dai ya manta da Katsina, domin dama shi dan Daura ne. Mun kuma san tsamar da ke tsakanin biyun a tarihi. To in ba haka ba, ya kamata a kawo qarshen rashin albarkar da ake a qauyukan Katsina. Jiya a Wurma, Kurfi local government, an kwashe mutanen da ba a san adadinsu ba. Satin da ya wuce a Jibia an yi makamancin haka. An saba dama a nan yankin, tsakanin Batsari, Safana da Jibian. Dauki dai-dai yayi yawa a yankunan. Abin haushin shine, sai an yi operation din an gama da awanni, sai sojoji su zo suna muzurai suna kyarar jama’a. Allah ya sauqe!

Baba ya rufe bodojin yankin. Ba shiga, ba fita. Harkokin neman abincin yankin sun tsaya. Har a nan Kano, yan kasuwa suna ta qorafi saboda an hana kostomas tsallakowa daga qetare. Ka yi hira da yan Kasuwar Sabon Gari ko Kwari. Jama’a, cikin qasa da sati daya da wannan total garqame boda, sun fara galabaita. Abin mamaki, a jahar shugaban qasa ake da sansanin yan gudun hijira. Qauyukan da aka tasa suna da yawa. Kullum kuma qaruwa suke. Abin haushin shine, sojojin sai dai su tare mu a kan titi su yi mana wulaqanci ko mu Jefa musu naira 50, 100, kai ko 20 ma.

A wannan lokacin, babu maganar jam,iyya ko wani 6angaranci. Wallahi idan bamu tashi tsaye ba, wajen gayawa Baba gaskiyar abinda yake faruwa, wallahi gaba daya zamu halaka. Misali, an hana shigo da abinci gaba daya, saboda a inganta noman cikin gida. Shekaran jiya, a Magama restaurant, Katsina, na hadu da wani attajirin abokina wanda ya rantse da Allah cewa, shekara 3 da ta wuce, yana iya noma, a qalla, buhu 500 na dankali a wannan yankin na jibia. Amma yanzu an tashi qauyen da yake noman. Irinsa-irinsa suna da dinbin yawa. A qarshe duka sai dai mu koma bara in ba a samar da zaman lafiya a wannan yankin ba.

Ya Allah ka sanya tausayi a zuciyar shugaba Buhari. Ya Allah ka bashi hikimar warware wannan matsalar. Ya Allah ka jiqanmu, ka tausaya mana, ta hanyar saita qwaqwalwar shugabanmu! Ameen!

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan