Tsakanin Aikin Fassara da Aikin Tafinta

123

Abu mai sauki ne wanda ya iya wasu yaruka ya iya aikin “tafinta” (interpretation) amma ba kowa ne don ya iya yare fiye da daya ba ya kasance ya iya “fassara” (translation).

Aikin tafinta ya danganci magana ce ta fatar baki kadai, wato a yi magana da baki cikin wani harshe, shi kuma tafinta ya fade ta cikin wani harshen daban domin cimma wata fahimta. Ita kuwa fassara a kaso ma fi yawa ta ta’allaka ne akan rubutu.

Aikin fassara fage ne guda daga cikin fagagen ilimi da ake da su a duniya, wanda ake koya a kuma koyar da shi karkashin wasu dokoki na musamman kamar dai kowanne fanni na ilimi.

Ba daidai bane don mutum ya iya harshe fiye da daya, ya dauka zai iya yin aikin fassara tsakanin wadannan harsuna ba tare da sanin ilimin fassara ba. Akwai dokoki da dama da mai bukatar yin fassara ya kamata ya sani, kadan daga cikinsu su ne:

Kasantuwar fassara fasaha ce ta mayar da wani zance da aka fada ko aka rubuta daga wani harshe zuwa wani ba tare da canza ma’anarsa ba. Ana yin fassara cikin harsuna da dama, wato daga wani harshe zuwa wani.

Ire-iren fassara ya danganta da abin da aka nufaci a fassara, misali, duk abin da za a fassara shi na fannin addini, da kimiyya da shari’a za a fassara su ba tare da sake musu tsari ba. Ana kiran wannan nau’i na fassara da “fassara ta kai-tsaye”.
Akwai kuma fassara da ake yinta ta hanyar kawo fahimtar mai fassara, wato mai fassara zai karanta sannan ya fassara shi yadda ya fahimta, ba tare kuma da ma’ana ta canja ba, misali fassarar wani labari ko bayani, da irin fassarar da ‘yan jaridu suke yi.

Akwai tubalan ginin fassara da ya zama wajibi mai fassara ya kula da su yayin aiwatar da aikin fassara.

1- Nakaltar Harsuna
Wajibi ne mai fassara ya nakalci harsunan da zai yi amfani da su wajan fassara. Misali, idan za a fassara wani abu daga Turanci zuwa Hausa, dole sai an nakalci wadannan harsuna yadda ya kamata.

2- Nakaltar al’adu
Tilas ne ga mai fassara ya nakalci al’adun mutanen da yake fassara a harshensu, domin gujewa samun tangarda da sauran matsloli da harshe zai iya jawowa.

3- Bincike
Wajibi ne mai fassara ya kasance mai bincike akan sassan ilimi, da yin tambayoyi ga kwararrun masana a fagen ilimi don ya samu yin fassara sahihiya kuma ingantacciya. Misali, idan za a yi fassara a fannin ilimi kamar fagen kimiyya, magunguna, kere-kere ko shari’a to sai ya tuntubi masana a wannan fanni domin su taimaka wajan fassara kalmomin da suka shafe su.

5- Kamus
Akwai bukatar mai fassara ya mallaki kamus na harsunan da yake fassara a cikinsu, misali, idan yana yin fassara ne daga Turanci zuwa Hausa to sai ya mallaki Kamus na Turanci dana Hausa.

Dadin dadawa, akwai matakai da mai fassara zai bi domin cimma fassara ingantacciya. Daga cikin wadannan matakai akwai:

Mai fassara ya karanta abin da zai fassara karatu na nutsuwa da fahimta, har sai ya tabbatar ya fahimci komai da komai na abin da zai fassara din.

A guji yin fassara ta kalma da kalma ko jimla da jimla, domin kowanne harshe yana da tsari nasa na daban.

A guji yin fassara ta karya, domin hakan babban laifi ne, duk abin da za a fassara a tabbata gaskiya aka fada domin gujewa matsalolin da fassarar karya ka iya jawowa.

A fassara fannonin da suka shafi addini, shari’a, kimiyya da sauransu, kamar yadda suke ba tare da an canja komai nasu ba, wato ba tare da amfani da ra’ayin mai fassara ba.

A yi fassara cikin sasaukan harshe don gujewa bacewar ma’ana ta hanyar amfani da kalmomi ko jimloli ma su wahalar ganewa.

A kula, aikin fassara aiki ne da yake bukatar kaffa-kaffa, da kwarewa kafin a aiwatar da shi. Akwai matsaloli da dama da gurbatacciyar fassara ke iya jawowa ga tattalin arzikin kasa, tsaro, lafiya da dukiyoyin al’umma. Babban nauyi ne akan NITI (Nigerian Institute of Translators and Interpretors) da ta tabbatar da dakile masu yiwa fassara hawan kawara a Nigeriya. Ya kamata NITI ta karfafa tsarin bada lasisi (license) da kuma tabbatar da amfani da shi ga duk wanda aka amince ya gudanar da aikin fassara. A kuma gargadi jama’a da su gujewa ‘yan fassarar bigi-bagiro da ‘yan shaci-fade, a tabbatar da doka da zata hukunta wanda aka kama suna yin fassara wala’alla kamfani ne ko kungiya ko a daidaikun mutane ba tare da sahalewar hukumar fassara da tafinta ta kasa ba. Hakan zai taimaka wajan tsaftace aikin fassara da tabbatar da shi akan tsari da rage matsaloli masu yawa da harshe ka iya jawowa sakamakon gurbatacciyar fassara kamar yadda kowacce kasa da ta san darajar kanta take yi.

Daga: Aysha Bilkisu Umar.

Daliba a sashen kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero dake Kano.
27/8/19.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan