Abinda Yasa Muka Rufe Iyakar Najeriya Da Benin- Buhari

200

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce abinda yasa aka rufe bodar Najeriya da Benin na wucin gadi shi ne yawan shigo da kaya ta ɓarauniyar hanya, musamman shinkafa da ake yi bakin iyakar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa rufe kan iyakar Seme ta Najeriya da Benin ya biyo bayan wani aikin haɗin gwiwa na tsaron kan iyaka da gwamnati ta bada umarni, dake da manufar tsare iyakokin Najeriya na ruwa da na teku.

Aikin tsaron bakin iyakar, da aka yi wa laƙabi da ‘Ex-Swift Response’, ana gudanar da shi ne da haɗin guiwar jami’an Hukumar Hana Fasa Ƙwauri, Hukumar Kula da Shige da Fice, jami’an ‘yan sanda da na soji, bisa kulawar Ofishin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro.

Shugaban na Najeriya bada wannan dalilin ne a yayin wata ganawa da ya yi da takwaransa na Benin, Patrice Tolon, a wajen Taron Ƙasa da Ƙasa na Ci Gaban Afirka na Tokyo Karo na Bakwai, TICAD7 a Yokohama ranar Laraba.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja cewa Shugaba Buhari ya damu sosai bisa yadda ake shigo da shinkafa ta ɓarauniyar hanya.

Shugaban ya ce aikace-aikacen masu shigo da kayan ta ɓarauniyar yana yin barazana ga matakin iya ciyar da kai da Najeriya ta riga ta kai tuni.

“Yanzu da mutane a yankunan karkara suke komawa gonaki, kuma ƙasar ta ajiye kuɗi masu kauri da waɗanda da tuni an yi amfani da su wajen shigo da shinkafa ta hanyar amfani da ɗan asusunmu na ajiyar ƙasashen waje, ba za mu bari a ci gaba da shigo da kaya ta ɓarauniyar hanya ba”, in ji Shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya ce rufe bakin iyakar Najeriya ta Yamma da aka yi an yi ne don a ba hukumomin tsaron Najeriya dama su samu wata dabara da za su daƙile wannan abu mai hatsari da irin illolinsa masu faɗi.

Da yake mayar da martani ga tarin matsalonin da Shugaba Talon ya ce rufe bakin iyakar ya jawo, Shugaba Buhari ya ce ya lura da haka, kuma zai ƙara duba yiwuwar sake buɗe kan iyakar nan gaba kaɗan.

Amma, ya bayyana cewa zai yi wani taron tattaunawa da takwarorinsa daga Jamhuriyar Benin da Nijar don fito da matakai masu tsauri kuma na bai ɗaya don yin maganin yawaitar shigo da kaya ta ɓarauniyar hanya tsakanin iyakokin nasu.

Tun da farko, Shugaba Talon ya ce ya kai wa Shugaban Najeriya ziyara ne sakamakon tsananin wahalar da rufe bakin iyakar yake yi wa al’ummarsa.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu, musamman kisan ‘yan Najeriya da ake yi a Afirka ta Kudu

“Za a tattauna batun sosai a yayin ziyarar aiki da Shugaban Najeriya zai kai Pretoria a watan Oktoba, 2019”, in ji Mista Adesina.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan