An Yi Garkuwa Da Ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello

196

A ƙalla ɗaliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria masu garkuwa da mutane su ka yi garkuwa da su akan hanyar Kaduna zuwa Abuja
Tun da farko dai ɗaliban da ke shekararsu ta ƙarshe a tsangayar aikin lauya na jami’ar, an yi garkuwar da su a wani yanayi da har yanzu jami’an tsaron ƴan sanda ba su kai ga bayyana ainihin yadda abin ya kasance ba.
Idan za’a iya tunawa dai hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane tare da buƙatar kuɗin fansa, domin ko a watan Aprilu sai da aka yi garkuwa da shugaban hukumar ilimi ta bai ɗaya Mahmood Abubakar tare da ƴarsa akan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan