Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun tseratar da ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello, ABU dake Zariya da aka sace ranar Litinin da ta gabata a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Yakubu Sabo, ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Larabar nan a Kaduna cewa amma har yanzu masu garkuwa da mutanen suna riƙe da wasu sauran mutanen uku.
“Rundunar tana so ta bayyana cewa, a wannan rana ta 26 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 6:50 na yamma, wasu mutane ɗauke da makamai da kayan sojoji suka tsayar da wasu masu wucewa a mota a kusa da ƙauyen Masari a kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Abuja suka buɗe wa abubuwan hawa wuta, a sakamakon haka, suka yi garkuwa da mutum shida. Amma, sakamakon zafin nama da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka yi zuwa wajen da abin ya afku, masu garkuwa da mutanen sun saki mutum uku daga bisani, sakamakon tsinke da jami’an tsaro suka yi wa yankin”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce an tafi da ɗalibai ukun tare da motocin da aka bari a wajen da abin ya afku zuwa Ofishin ‘Yan Sanda.
Ta tabbatar da cewa Sashin Yaƙi da Garkuwa da Mutane, Sashin PMF da IRT na ci gaba ƙoƙari don tseratar da sauran mutanen uku tare da kama masu garkuwar.
“Rundunar tana son al’umma su lura da cewa, yayinda take alhinin abin da ya faru, labarin da ake yaɗawa a Intanet zugugutawa ne da kuma cakuɗa ƙarya da gaskiya, da nufin ƙara wa jama’a tsoro.
“Saboda haka, Rundunar tana kira ga jama’a da su yi watsi da irin waɗancan rahotonni masu rikitarwa.
Saboda haka, ya kamata ‘yan jarida su ci gaba da riƙe tarbiyyar sana’arsu.
“Rundunar tana roƙo da a riƙa tabbatar da laifuka kafin a wallafa don kauce wa ƙarya.
“Masu amfani da Intanet ma ya kamata su riƙa lura wajen yaɗa labaran da ba su da sahihanci a kafafen sada zumunta”, in ji sanarwar.
[…] Muƙalar Da Ta Gabata‘Yan Sanda Sun Tseratar Da Wasu Ɗaliban ABU Da Aka yi Garkuwa Da Su […]