Na Mayar Da Shehu Sani Marubuci A Fesbuk, Sule Hunƙuyi Kuma Ya Yi Gudun Hijira – El-Rufai

139

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai ya bayyana cewa ya mayar da tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani mai sharhi a kafafen sada zumunta, shi kuma Sanata Sule Hunkuyi ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Sin bayan da gwamnan ya yi masa ritaya daga siyasa.


Gwamna El-rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin Kpop Ham Malam Danladi Gyet na Ƙaramar hukumar Jaba a gidan gwamnatin jihar Kaduna.


“Mun cire Shehu Sani daga da’irar siyasar jihar Kaduna, in da yanzu ya koma mai rubutu a kafafen sada zumunta, shi kuma Sule Usman Hunƙuyi ya koma ƙasar Sin da iyalinsa duk da cewa sun yi wa harkar rancen da mu ka yi yunƙuri karbowa kafar ungulu duk da cewa zai bunƙasa rayuwar al’ummar jihar Kaduna”


El-Rufai ya ce naɗin Kpop Ham an yi shi ne a bisa cancanta da dacewa domin shi yana bayar da mukami ga waɗanda su ka ƙware duk da cewa ana ƙalubalantarsa akan yadda ya ke naɗa waɗanda ba ƴan jihar Kaduna ba.


“muna la’akari da mutane waɗanda su ka ƙware tare da sadaukarwa ga aiki. Dukkanin wani wanda muka naɗa mukami mun naɗa shi ne bisa cancanta” in ji El-rufai


A nasa ɓangaren Kpop Ham ya godewa gwamna El-rufai bisa yadda ya naɗa ƴan ƙabilar Ham maza da mata a cikin ƙunshin gwamnatinsa.


A ƙarshe ya buƙaci gwamnan da ya ƙarasa aiyukan da aka yi watsi da su a masarautar Ham domin hakan zai ƙarasa bunƙasa cigaban yankin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan