Virgil Van Dijk Da Allison Becker Sun Lashe Manyan Kyauta

166

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool mai tsaron baya wato Virgil Van Dijk ya lashe kyautar dan wasan baya wanda yafi kowa kokari a gasar zakarun nahiyar turai.

Ayanzu dai shekaru 10 kenan rabon da wani dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafan kasar Ingila ya lashe wannan kyauta inda tun a kakar wasan 2008 zuwa 2009 da dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea wato John Terry ya lashe.

A tarihi dai ‘yan wasan gasar Premier guda uku ne suka taba lashe wannan kyauta.

John Terry ya lashe sau 3.

Jaap Stam ya lashe sau 2.

Virgil Van Dijk ya lashe sau 1.

Shima mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wato Allison Becker ya lashe kyautar mai tsaron gidan dayafi kowa kokari a gasar zakarun nahiyar turai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan