Birnin Lagos Shi Ne Birni Mafi Haɗari A Duniya – Rahoto

382

Wani rahoto da cibiyar bincike akan tattalin arziki ta fitar ya bayyana birnin Legas a matsayin garin da yafi kowanne gari hadari a duniya.


Cibiyar ta kasar Birtaniya wacca ta gabatar da binciken akan birane guda sittin na duniya, wajen yin la’akari da tsaro, lafiya, kayan more rayuwa da sauransu.


Duk da cewa cigaba a fannin abubuwan more rayuwa yana da mutukar muhimmanci wurin ingancin rayuwar al’umma. Amma kuma mafi muhimmanci daga cikin ababen more rayuwa shi ne samar da tsaro ga al’ummar yanki da ‘yan kasuwa dama mutanen da su ke shigowa domin ziyara.


A ɗaya bangaren kuma birni Tokyo wanda shi me babban birnin kasar Japan ya Zama shi ne birni na daya da aka bayyana wanda yafi ko ina zaman lafiya a duniya. Sai kuma biranen Singapore, Osaka, Amsterdam da Sydney sune suka biyo bayan birnin na Tokyo.


Wannan shi ne karo na farko da garin na Legas ya fito a cikin jerin biranen, sai dai kuma ya zo a matsayin 56 a bangaren matsalar tsaro, sannan kuma yazo na 58 a bangaren rashin cigaba.


Madogara Shafin Legit Hausa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan