Kotu Ta Soke Zaɓen Ɗan Majalisar Takai Da Sumaila

239

A ranar Juma’a ne Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen dake zama a Kano ta soke zaɓen Shamsud’deen Bello Dambazau, ɗa ga Abdulrahman Dambazau, tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, a matsayin mamba mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Sumaila da Takai.

Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ta ba Surajo Kanawa, ɗan takarar jam’iyyar PDP Takardar Shaidar Lashe Zaɓe.

Shamsuddeen, wanda bai yi takara a zaɓen ba, amma ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani, ya samu damar zama ɗan majalisa ne bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a Kano ta hana tsohon dogarin Shugaban Ƙasa, Kawu Sumaila yin takara.

Farkon rikicin

Shamsuddeen ya maka INEC, jam’iyyar APC da Kawu Sumaila a kotu inda yake ƙalubalantar Kawu Sumaila a matsayin ɗan takarar APC.

Ya faɗa wa kotun, ta bakin lauyansa, Nuraini Jimoh, cewa Kawu Sumaila ya yi nemi takarar Sanatan Kano ta Kudu, amma Kabiru Gaya ya kayar da shi.

Haƙiƙa, Kawu Sumaila ya nemi takarar Sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar APC. Sanata mai ci, Kabiru Gaya ne ya kayar da shi.

Bayan nan ne sai Reshen Jam’iyyar APC ta Kano ya saka masa da takarar Majalisar Wakilai na Sumaila da Takai wadda ita ma take a Mazaɓar Sanata ta Kano ta Kudu.

Sakamakon haka ne APC ta ci zaɓen ɗan majalisar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan