Sana’ar rini wacce ta yi fice a ƙasar Hausa da sauran garuruwan Hausawa sana’a ce da ta zamo ginshikin samun abinci ga masu yin ta tare da magance musu matsalolin rayuwa na yau da kullum.
Sai dai kuma sana’ar a birnin Kano ta shahara matuƙa, domin wannan sana’a, wacce masu yin ta suka ce ta faro ne kusan shekaru 700, ta zamo ginshikin samun abinci ga masu yin ta.
Bugu da ƙari tarihi ya nuna marinar kofar Mata da ke cikin birnin Kano an fara rini a cikinta tun a cikin shekarar 1498.
Sai dai kuma wannan marina mai tsohon tarihi na fuskantar barazanar ɓacewa a doron ƙasa idan aka yi la’akari da yadda rijiyoyin da ake zuba baba fiye da guda 100 sun ɓace sakamakon yadda ƙasa da tarin shara ya cike su.
Baya ga cikewar rijiyoyin baba su ma masu yin sana’ar wato maruna na fama da rashin isasshen jari tare kuma rashin masu sanya jari daga ƙasashen waje.
A ɗaya bangaren kuma sana’ar tana samun koma baya la’akari da yadda ake samun ƙarancin masu siyan kayayyakin da ake saya tare kuma da yadda marinan ke zargin ƴan ƙasar sin wato Chana ke musu satar fasaha
Akwai buƙatar mahukunta su kai dauki cikin wannan sana’a mai tsohon tarihi domin tserewa faɗawa jerin tarihin durƙushewar masana’antu a jihar Kano