Ministan Wasanni Sunday Dare Ya Taya Najeriya Murna

33

Sabon ministan wasanni na kasar nan wato Sunday Dare Ya taya ‘yan wasan motsa jiki na kasar nan bisa nasarorin da suka samo a gasar motsa jiki ta nahiyar Afrika da aka kammala a kasar Morocco.

Najeriya dai ta lashe kyaututtuka guda 127, inda suka lashe Zinare 46 da Azurfa guda 33 da kuma Tagulla 48.

Najeriya dai sun kasance a matsayi na biyu a wannan gasa inda kasar Masar suka kasance a matsayi na 1.

Najeriya dai sun dade basuyi irin wannan kokarin ba a gasar motsa jiki ta nahiyar Afrika ba kamar wanne lokaci.

A dalilin wannan kokari da sukayi ne ministan wasannin na kasa ya tayasu murna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan