Shaiɗan Ya Biyomu Bayan Da Muka Yi Jifa –Hajiya Jamila Mai Wuƙa

207

Wata sabuwar Hajiya data sauke farali a bana Hajiya Jamila Ado Maiwuka ta bayyana cewa babu shakka shaidan ne ya biyosu a bayan da suka gudanar da jifan shaidan a can kasar Saudia, a wata tattaunawa da tayi da jaridar WhiteBlood


Hajiya Maiwuka ta bayyana cewa jim kadan bayan sun dawo masauki daga jifan shaidan kawai sai fada ya dinga barkewa tsakanin mahajjata, domin kuwa a inda suka sauka hawa na 5-7 duk rigima aka dingayi, hatta ita kanta tace sai da suka raba raini da wata, hakan yasa sukayi tsammanin kodai shaidan ne ya biyosu masaukin don ya rama jifan da suka yi masa.


Maiwuka ta kara da cewa babban abinda yafi bata mamaki shi ne yadda mahajjata tsofaffi musamman Fulani ke kaffa-kaffa da kudaden guzurinsu domin gudun ‘yandamfara amma duk da haka sai da aka samu wadanda suka dinga wankarsu.

WhiteBlood Media

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan