Abubuwan Da Suke Kawo Tashin Hankali A Gidajen Aure

262

Gabatarwa

Da farko dai faɗa a gidajen aure abu ne wanda ya daɗe yana haddasa rabuwar aure.

Abinda ake nufi da faɗa a gidajen aure, ana nufin hayaniya da rikici da ake samu tsakanin miji da mata a bisa wasu abubuwa da sukan taso.

Wannan yawan faɗa yana haifar da matsaloli da yawa musamman ma a ce ma’aurata suna da yara waɗanda suka haifa. Wannan ya kan shafi yaran ta hanyoyi da dama, saboda binciken da aka yi ya nuna cewa yaran da suke yawan ganin iyayensu na faɗa suna yawan samun kan su a cikin damuwa koda sun je makaranta, kuma ba sa iya mayar da hankali a karatu.

To, a nan, zan kawo abubuwan da suke haifar da waɗannan matsaloli da kuma yadda za a magance su.

Mene ne yake kawo rikici a zamantakewar aure?


Abubuwan da suke jawo rikici a zamantakewar aure ba wasu baƙin abubuwa ba ne, abubawa ne waɗanda suke fitowa ƙururu. Idan muka kalli tsarin neman aure a ƙasar Hausa, za mu ga cewa ma’aurata suna haifar wa kansu matsala tun kafin aure duba da yadda tsarin neman auren yake. A ƙasar Hausa, wasu shekaru baya da suka gabata, ana tsarin neman aure ne dai-dai ƙarfin miji, haka yanzu zamani ya zo mutane suna neman auren da ya fi ƙarfinsu.

Idan muka yi la’akari da yadda tsarin tattalin arziƙin kowanne mai neman aure yake, za mu iya cewa kowa ya yi dai-dai ruwa dai-dai tsaki domin kuwa a wani nazari da masani Karl Marx ya yi, ya raba al’umma kashi uku inda ya kira su da Upper Class, (Ajin Sama) Middle Class (Ajin Tsakiya) da kuma Lower Class (Ajin Ƙasa), hakan yana nuna mana a cikin kaso 100% kaɗan ne daga cikin waɗanda suke a Upper Class kuma su auri Lower Class, a zauna lafiya. Duba da yanayin buƙatun mata na yau da kullum.

Haka kuma, tsarin zamantakewar aure, zai fi kyau, a ce akwai fahimtar juna a tsakani da gaskiya, da ba wa kowa haƙƙinsa kamar yadda al’umma, al’ada da addini sukaa ɗora musu. Domin kuwa, idan aka kare wannan hakkin za a samu zaman lafiya a gidan aure. Kamar yadda kowa ya sani, ana samun tsarin zamantakewa na rayuwar ɗan Adam (Social Change), ni abinda na fahimta Social Change fita daga duhun kai, duba da a baya babu yawaitar ilimi kuma kowa yana zaune lafiya babu yawan faɗace-faɗace a gidajen aure, yanzu kuma ga ilimi ya shiga ko’ina, al’umma kuma tana ƙara shiga daji.

Akwai wasu nazarce-nazarce da na yi a kan shan miyagun ƙwayoyi da fyaɗe, a kan me yake kawo su, sai na fuskanci cewa ai faɗace-faɗace a gidan aure, shi ne kusan abinda yake kawo matsalolin ba talauci ba kamar yadda koyaushe ake magana. Sai na kalli yadda iyaye mata aurensu yake mutuwa bayan sun samu yara a tsakani, yaran da ake bari suna rayuwa ne a tsakanin ko a hannun matar uba, wanda na tabbata babu wata kulawa da za su samu, ko kuma a sake su suna garari a kan titi babu maganar makaranta ko me za su ci, ko kuma a gaban kaka wadda ita kuma ta yi wahala da babansa, shi ma ta zo za ta yi wahala da shi. “Ba za ta saɓu ba, bindiga a ruwa”. To, matakin lalacewar al’amura mataki na farko kenan.

Bayan haka sai na yi wani dogon tunani, na gano cewa, ai kowace al’umma tana da dokokinta na zamantakewa, kuma kowace, al’umma tana da al’adarta.

Tambayar da na yi wa kaina ita ce, shin dokokin ba a aiki da su ne ko kuma? Muna ganin koma bayan da al’ummarmu take samu shi ne ci gaban, ina al’ada ana amfani da ita ne wajan bikin Salla kawai ko kuma ita ta zama (Mothers’ Day), da Arabian Night?

In shaa Alla zan ci gaba da wannan nazari domin fitar da aya daga tsakuwa.

Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Saƙo kawai)

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan