Home / Cigaban Al'umma / Za A Fara Koyar da Fulatanci A Makarantun Zamfara- Matawalle

Za A Fara Koyar da Fulatanci A Makarantun Zamfara- Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa za ta shigo da harshen Fulatanci a manhajar makarantunta a daidai lokacin da za ta fara samar Rugage 300 a wannan mako.

Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne a Gusau lokacin da ya karɓi tsarin gina Ruga na jihar daga wani masanin tsarin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa tuni Gwamnan ya sanar da share hekta 100 a kowace ɗaya daga cikin mazaɓun sanatoci uku na jihar domin shirin Rugar na gwaji.

Yayin gabatar da tsarin gina Rugagen, Sarkin Mafara, Muhammad Barmo, wanda ya yi magana a madadin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, ya roƙi Gwamnatin Jihar da ta sa harshen Fulatanci a manhajar makarantunta.

Sarki Barmo ya lura da cewa tunda ba za a iya raba al’ummar Hausawa da na Fulani ba, kuma tuni ana koyar da harshen Hausa a makarantu, ya kamata shi ma a koyar da Fulatanci.

Daga nan sai Gwamna Matawalle ya umarci Ma’aikatar Ilimin Jihar da ta fara aiki cikin gaggawa don shigar da Fulatanci a manhajar makarantun.

“Wannan zai bunƙasa amfani da harshenmu na gida ga al’ummomi masu zuwa.

“Tunda mun yi alƙawarin gina makarantun firamare da sakandire a sabbin Rugagen da za a samar, za mu tabbatar da cewa ba a manta da harshen gida ba”, a cewar Gwamna Matawalle.

NAN ya kuma ruwaito cewa dama tuni Gwamnan ya sanar da cewa za a fara kafa Rugagen ne a yayin bikin cikar sa kwana 100 a ofis.

Ya ce Gwamnatin Jihar za ta tabbatar da kammala kafa Rugagen a kan lokaci kafin Gwamnatin Tarayya ta fara nata shirin Rugar a jihar.

Gwamna Matawalle ya yi alƙawarin samar da hanyoyin kiwo na zamani a Rugagen, abinda zai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mazauna Rugar, tare da bunƙasa tattalin arziƙinsu.

About Hassan Hamza

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *