Za Mu Ɗauki Mataki Akan Raina Ƴan Arewa A Lagos – Ashiru Sharif

182

Gamayyar kungiyoyin al’ummar arewacin kasar nan sun bayyana matakin da gwamnatin jihar Lagos ta dauka na tsare wasu matasayan jihar Jigawa da suka je ci-rani a jihar a matsayin cin zarafi kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan.


Ashiru Sharif shi ne shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin, ya shaidawa gidan rediyon BBC cewa gazawar shugabanni wajen kare hakkin `yan arewa ce ke ja wa ‘yan arewa wulakanci.


Ya ce “Da suka binciki mutanen nan ba su kama su da laifi ba, mene ne dalilin tozartar da su a jera su a layi ana daukan hotonsu ana maganganu?”


Kungiyar ta nuna cewa tafiyar mutanen a cikin kungiya manuniya ce kan cewa ba su da wata mummunar nufi a tattare da su.


Ashiru Sheriff ya ce a yanzu za su dauki mataki, za su bukaci a dawo da duk wasu damammaki da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa al’ummar Arewa, wadanda aka danne.


Wadannan damammaki sun hada da kason guraben ayyukan yi da ake bai wa al’ummar wurin da aka kafa kowane kamfani.


Ya ce za su tabbatar an yi doka a dukkanin jihohi 19 na Arewacin kasar wadda za ta tabbatar da cewa ana bai wa ‘yan asalin jihar da aka kafa kowane kamfani kaso 70 cikin 100 na ma’aikatan da za a dauka.


Hakan a cewarsa zai samar da ayyukan yi ga matasa, sannan ya fitar da su daga dabi’ar shan miyagun kwayoyi da dabanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan