Ana Ci Gaba Da Kashe ‘Yan Ƙasashen Waje A Afirka Ta Kudu

149

‘Yan sanda sun ce an kashe mutum biyar ranar Talata a Afirka ta Kudu, yayinda Shugaba Cyril Ramaphosa ya lashi takobin kawo ƙarshen hare-haren, Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka, AU da Najeriya kuma suka tsawatar.

Wasu gungun mutane- masu ɗauke da gatari da takubba, suka tattaru a babban wajen kasuwanci dake Johannesburg a rana ta uku da fara hare-haren da ake kai wa baƙi, sa’o’i kaɗan bayan wasu mahara sun ƙona tare da kwashe kaya a garin Alexandra, abinda ya tilasta ‘yan sanda su harba harsasun roba don tarwatsa su.

An kashe mutane biyar, yawancin su ‘yan Afirka ta Kudu, a cewar ‘yan sanda, suna masu ƙarawa da cewa an kama mutum 189.

A wani jawabin faifan bidiyo da aka yaɗa a Twitter, Shugaba Ramaphosa ya ce hare-hare a wuraren kasuwanci “da ‘yan ƙasashen waje wani abu ne da kwata-kwata ba za amince da shi ba, wani abu ne da ba za mu bari ya ci gaba da faruwa a Afirka ta Kudu ba”.

“Ina so a dakatar da hare-haren”, in ji Shugaba Ramaphosa, yana mai ƙarawa da cewa “babu wata hujjar kai hare-haren”.

Hare-haren kan mai uwa da wabi da ake kai wa kan shaguna da kamfanoni mallakin baƙi ‘yan ƙasashen waje yana da tsohon tarihi a Afirka ta Kudu, inda ‘yan ƙasar da dama ke zargin ‘yan ci rani da haifar da rashin aikin yi, musamman sana’ar hannu.

Afirka ta Kudu wani babban waje ne da masu hijira saboda dalilan tattalin arziƙi daga maƙwabtan ƙasashe, Lesotho, Mozambique da Zimbabwe ke yada zango.

Sauran sukan zo ne daga ƙasashe masu nisa kamar Kudancin Asia da Nigeria, ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka.

Amma hare-haren da ake kaiwa a wannan mako sun ƙaru sosai fiye da da, koda yake dai ba a san mene ainihin dalili ba.

“Sun ƙona komai”, wani mai shago ɗan Bangladesh, Kamrul Hasan, ɗan shekara 27 ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP haka a Alexandra, yana mai ƙarawa da cewa a kan kai wa kantinsa hari duk bayan wata uku zuwa shida.

“An kwashe kuɗina kaf. Idan Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta biya min kuɗin tikitin jirgi, zan koma Bangladesh”, in ji shi.

Alexandra, ɗaya daga cikin birane mafiya talauci a Afirka ta Kudu, yana da nisan kilomita biyar ne (mil uku) daga Sandton.

Gwamnatin Afirka ta Kuduta ta ce ranar Litinin an cafke fiye da mutum 90 dake da alaƙa da hare-haren da sace kaya a kantina da kamfanoni a Johannesburg da wuraren dake kewaye.

An samu irin waɗannan hare-hare a babban birnin ƙasar, Pretoria, ranar Litinin lokacin da kafafen watsa labarai na ƙasar suka bada rahotannin cewa kantina suna cin wuta a Marabastad- wani babban wurin kasuwanci da yawanci masu gudun hijira ta tattalin arziƙi ke da zama.

Tuni dai Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta aika da tawagar ta musamman don tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu bisa yadda za a kawo ƙarshen kisan ‘yan Najeriya da ake yi a ƙasar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan