Masu Horas Wa Guda 3 da FIFA Ta Ware Domin Fitar Da Gwarzo

166

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta fitar da jerin masu horas wa guda 3 dazata zabi wanda yafi bajinta acikinsu.

Saidai wani abin mamaki wadannan masu horas wa daga kasar Ingila suke inda suke horas da kungiyoyin kwallon kafa ta Ingila.

Ga masu horas war kamar haka:

  1. Pep Guardiola da asalin kasar Spain wanda yake horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City inda shine ya lashe duk wasu kofuna na kasar Ingila na kakar wasan data gabata ta 2018 zuwa 2019.
  2. Jürgen Klopp dan asalin kasar Germany kuma mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kuma wannan mai horas wa shine ya lashe gasar zakarun nahiyar turai sannan kuma ya lashe Super Cup.

Mauricio Pochettino dan asalin kasar Argentina kuma mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur dake kasar Ingila sannan shine yakai Kungiyar wasan karshe duk da sunyi rashin nasara a hannun Liverpool.

Shin ko waye zai lashe wannan kyautar acikinsu duba da cewa kowa yayi kokari?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan