Ministar Kuɗi Ta Bayyana Lokacin Da Za A Miƙa Wa Majalisa Kasafin Kuɗin 2020

177

Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙarin miƙa kasafin kuɗin shekara ta 2020 ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa kafin ƙarshen watan Satumba.

Ministar, wadda ta yi jawabi a wani taron tattaunawa na Shirin Tsara Karɓar Taimako na Ƙasa a Abuja ranar Laraba ta ce tuni an fara shirye-shiryen miƙa kasafin kuɗin 2020, tare da fara tsare-tsare a kan lokaci.

Ministar ta kuma fito da wasu ɓangarori 11 na tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta mayar da hankali a kai.

Wuraren da za a bada fifikon, a cewar Ministar, sun haɗa da gyaran tattalin arziƙi da na shugabanci, waɗanda za su mayar da hankali kan saita ƙananan sana’o’i ta hanyar manufofin tattalin arziƙi, kuɗi, kasuwanci da kyakkyawan shugabanci.

Sauran ɓangarorin sun haɗa da haɓɓaka zuba jari a kayayyakin more rayuwa, gina ɗan Adam don samar da ayyuka da haɓaka tattalin arziƙi, inganta lafiya, ilimi da ƙwazon aiki ga ‘yan Najeriya.

Ta ce tsarin ya haɗa da tabbatar da samar da makamashi da lantarki da albarkatun man fetur; inganta tsarin sufuri da sauran abubuwan more rayuwa, da ciyar da masana’antu gaba, su kuma su mayar da hankali a kan ƙanana, ƙananan kamfanonin da matsakaita.

Ministar ta kuma bayyana samar da ingantaccen tsaro ga dukkan ‘yan ƙasa, inganta aikin gona ta yadda za a iya ciyar da kai, don samun tsaron abinci, inganta walwalar jama’a ta hanyar haɓaka zuba jari a bangaren walwalar jama’a da kuma bada damar samun gidaje ga gagarumin shirin samar da gidaje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan