Siyasa: Ko Ina Bamanga Tukur Ya Shiga?

147

Sunan Alhaji Bamanga Tukur ba ɓoyayyen suna bane a da’irar siyasar ƙasar nan, domin sunansa ya fara shahara ne a cikin shekarun 1983 a lokacin da aka zaɓeshi a matsayin gwamnan jihar Gongola.


Sunan Bamanga Tukur ya ƙara fitowa sarari a siyasar ƙasar nan bayan da ya fito takarar shugabancin ƙasar nan a shekarar 1992 duk da cewa bai kai labari ba.


Gwamnatin soji ta marigayi janaral Sani Abacha ta naɗa Bamanga Tukur a matsayin ministan ciniki da masana’antu.


A cikin watan Maris na shekarar 2012 ne wakilan jam’iyyar PDP su ka zaɓi Alhaji Bamanga Tukur a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, ɗaukacin ‘yan takaran dai sun janye wa Bamanga gabanin kaɗa ƙuri’a.


Lokacin da ya samu kansa bisa kujerar mulkin PDP, sai ya fara zama zaki, ya dauki turbar tankwasa gwamnonin jam’iyyarsa domin su amince da takarar Jonathan a karo na biyu. Wanda hakan ya haifar da rikicin da ake gani Bamanga Tukur ne silarsa.


Bisa wannan dalili ne Bamanga Tukur ya fara fuskantar matsin lamba akan lallai sai ya sauka daga kan shugabancin jamiyyar PDP, sabo da yadda ya nuna lallai ya zama ɗan amshin shatan shugaba Goodluck Jonathan.


Duk da ya kai shekaru tamanin a duniya, ya yi zaton yana da sauran karsashin da zai yi wa Shugaban kasa hidima, ya zama ɗan amshin Shatansa, duk kuwa da cewa al’ummar kasa ba su amince da hakan ba.


A lokacin yana shugabancin jamiyyar PDP ya yi tasiri sosai, domin sai da ya kai ga dakatar da wasu gwamnoni, ya kuma kori wasu daga jam’iyyar.


Sai dai kuma Jam’iyyar PDP ta fuskanci matsalolin cikin gida a karkashin mulkin Alhaji Bamanga Tukur abinda ya haddasa ballewar wasu gwamnoni biyar da ‘yan majalisar wakilai da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta APC.

A cikin watan Janairu na shekarar 2014 Alhaji Bamanga Tukur ya rubuta takardar murabus daga shugabancin jamiyyar PDP, bayan matsin lamba da ya dinga fuskanta daga wasu jiga-jigan jam’iyyar.


Tun bayan murabus din da ya yi aka daina jin muryarsa a harkokin siyasar ƙasar nan, sai dai an ji yo amonsa a cikin watan Satumba na shekarar 2015 a gurin taron cikarsa shekaru 80 a duniya ya bayyana cewa ya fice daga harkokin siyasar ƙasar nan. Bisa dalilin cewa yanzu lokaci ne da ya kamata ya huta domin bai wa sabbin-jini damar taka tasu rawar a harkokin siyasar ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan