A jijjifin safiyar Larabar nan ne Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Fintiri ya kusa rasa ransa lokacin da waɗansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari wajen da jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna Jihar Kogi.
Gwamna Fintiri shi ne ya jagoranci zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP da aka gudanar a Filin Wasa na Confluence Stadium dake Lokoja, babban birnin jihar.
Kaɗa ƙuri’a da ƙirga ƙuri’un ya kai wakilai har safiyar Laraba.
Wakilin jaridar The Punch, wanda ya shaida yadda abin ya faru, ya bada rahoton cewa ana cikin ƙirga ƙuri’u ne da aka fara da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Talata, sai ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a wajen, suka fara harbi kan mai uwa da wabi lokacin da Gwamna Fintiri ke ƙirga ƙuri’u.
Akwai akwatina goma ne waɗanda ake warewa tare da ƙirga ƙuri’un dake ciki, Gwamna Fintiri yana kan akwati ta takwas da misalin ƙarfe 1:15 na dare lokacin da aka fara harbe-harben bindigar.
Cikin gaggawa jami’an tsaron Gwamnan suka ɗauke shi, daga bisani kuma suka fitar da shi daga Filin Wasan da misalin ƙarfe 3:00 na dare.
Koda yake dai ba a iya tabbatar da adadin ‘yan bindigar ba, wani jami’in tsaro, wanda ya ɓuya a cikin wata mota ƙirar SUV mallakin ɗaya daga cikin masu buƙatar a tsayar da su takarar, ya ce sun kai mutum 20.
[…] Muƙalar Da Ta GabataYadda Gwamnan Adamawa Ya Sha Da Ƙyar A Wani Taron PDP […]