Ainihin Abinda Ke Faruwa Tsakaninmu Da TCN- KEDCO

127

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO, ya ƙaryata wani rahoton kafafen watsa labarai dake cewa abokan huɗdar KEDCO su sa ran ɗauke wuta a yankuna daban-daban.

A wata sanarwa da ta fito daga Shugaban Sashin Sadarwa na KEDCO, Ibrahim Sani Shawai kuma aka ba jaridar Economic Confidential a Abuja, kamfanin wutar ya ce babu batun tsayar da damar KEDCO ta yin kasuwanci a kasuwar wutar lantarki, yana mai ƙarawa da cewa manyan na’urorin da Kamfanin Tunkuɗo Wutar Lantarki, TCN ya yanke sun dawo aiki ka’in da na’in, kuma ana aiki da su yadda ya dace.

“Ma’aikatanmu suna nan suna ƙoƙari don tabbatar da cewa KEDCO ya alkinta wannan dama don ba abokan cinikinsa masu haƙuri wutar lantarki tabbatacciya, mai inganci kuma tsayayyiya a jihohi uku; Kano, Katsina da Jigawa”, in ji sanarwar.

“Kuma kamar yadda ake yaɗawa a wasu wurare cewa KEDCO ya samu matsala da TCN. Muna so mu bayyana a fili cewa ba mu da wata matsala da TCN. Duk mu biyun abokan aiki ne na ci gaba. Ya kamata a lura cewa dangantakarmu da TCN mai kyau ce, saboda haka, waɗanda ke da halayyar yaɗa jita-jita su zo su ji daga KEDCO cewa komai yana tafiya dai-dai, kuma muna yin aiki tare don cika alƙawarin Gwamnatin Tarayya na samar da wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

“Haka kuma, muna so mu faɗi a mahangar gaskiya cewa KEDCO mai bin doka ne kuma zai ci gaba da kasancewa a haka don tabbatar da cewa ɓangaren wutar lantarki ya samu ci gaba ta fuskar rarraba wutar lantarkin.

“Ba mu da dalilin da zai sa mu bijire wa dokar TCN saboda waɗannan dokokin ne ke yi mana jagora wajen tabbatar da kyakkyawar alaƙa tsakanin KEDCO da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren wutar lantarkin.

“Mun dawo aiki sosai, kuma mun shirya tsaf don ba abokan cinikinmu wutar lantarkin da suke buƙata ingantacciya kuma isasshiya.

“Nauyi ne da ya rataya a wuyanmu mu gamsar da abokan cinikinmu, kuma muna yin haka, kuma ta hanyar ƙara haɗawa, an zaburar da mu don mu ƙara gamsarwar da muke yi wa abokan cinikimu a halin yanzu.

“Saboda haka, muna kira ga TCN ya duba batun na’urar rarraba wutar lantarki mai nauyin MVA150 wadda ta daina aiki shekaru biyar da suka gabata don maye gurbinta da wata, don a guji nauyin wutar lantarki, kuma wannan zai ƙara mana ƙaimi mu ƙara ƙoƙari.

“Muna kuma gode wa ɗimbin abokan cinikinmu a jihohin Kano, Katsina da Jigawa bisa haƙurinsu da fahimta, kuma muna tabbatar musu cewa hakan zai ƙara wa KEDCO ƙaimi wajen inganta samar da wutar lantarki, da kuma gamsar da su bisa yadda muke rarraba wutar lantarki a jihohin da muke huɗda da su”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan