Ƴan Afirka 3 Da Su Ka Mallaki Sama Da Arzikin Rabin Al’umar Nahiyar

152

Mutane 3 a nahiyar Afirka da masu kudi suke kara arziki talaka na kara tsiyacewa sun mallaki sama da dukiyar da kusan mutane miliyan 650 na nahiyar suke da ita.


Wani rahoto da cibiyar Oxfam dake Ingila ta fitar mai taken “Labarin nahiyoyi biyu” ya bayar da muhimmanci game da rashin adalci wajen samun arziki a Afirka inda wasu mutane 3 suka mallaki sama da arzikin da rabin mutanen nahiyar biiliyan 1,3 suke da shi.


An bayyana rahoton a wajen taron tattalin arzikin Afirka da aka yi a Afirka ta Kudu, kuma an fadi cewar mutanen 3 dake jerin sunayen mafiya kudi a duniya na mujallas Forbes wato Aliko Dangote, Nicky Oppenheimer da Johann Rupert sun mallaki dala biliyan 28,8.


Rahoton ya ce kaso 75 na masu kudin Afirka suna ajiya a kasashen waje wanda hakan yake janyowa nahiyar asarar dala biliyan 14 a kowacce shekara, kuma nahiyar na fama da matsalolin illolin mulkin mallaka da manufofin da ba sa nasara da IMF da Bankin Duniya suke kawo wa kasashen na Afirka.


Daraktan Oxfam Winnie Byanyima ya ce Afirka a shirye ta ke da ta habaka amma ba a lokacinda kadan ne daga cikin shugabanninta ne ba su da kudaden da suka wuce hankali ba, sai a lokacinda ta samu shugabannin da za su yi aikidon cigaban tattalin arziki.


Rahoton ya ce kaso 50 na al’umar Afirka talakawa sun mallaki dala biliyan 23 ne kawai.
Bankin Duniya kuma ya ce a shekarar 2030 kaso 87 na talakawan duniya za su kasance a wannan nahiyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan