Hukumar dake kula da buga gasar Laliga ta kasar Andalos ta dakatar da dan wasa Gareth Bale.
Inda hukumar ta dakatar dashi wasa daya sakamakon katin rashin da’a dayasamu wato jan kati a wasan da Real Madrid ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Villarreal wasan mako na 3 inda aka tashi kunnen doki.

Kuma a wasan dai Bale shine ya jefawa Real Madrid kwallayenta guda 2.
Yanzu dai ta tabbata Gareth Bale bazai buga wasan da kungiyar kwallon kafan ta Real Madrid zata fafata da Levante ba a filin wasa na Santiago a ranar 14 ga watan nan da muke ciki wasan mako na 4.
Turawa Abokai