Tsohon Shugaban Ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe Ya Mutu

185

Tsohon Shugaban ƙasar Zimbabwe kuma shugaba na farko bayan ƙasar ta Samu mulkin kai Robert Mugabe ya rigamu gidan gaskiya. Ya mutu yana da shekaru 95 a duniya.
Robert Mugabe ya mutu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya a ƙasar Singapore, kamar yadda iyalansa su ka tabbatarwa da manema labarai.

Shugaba Mugabe ya hau mukin Zimbabwe a shekarar 1980 bayan karewar mulkin fararen hula marasa rinjaye, kuma matsalolin tattalin arziki da take hakkokin dan adam ne suka biyo bayan hawan sa mulki.


Mugabe ya dora alhakin tabarbarewar al’amura a kasarsa kan takunkuman da kasashen yammacin duniya suka saka musu, daga baya kuma sojoji suka tsoma baki a mulkin kasar, aka tsige shi tare da samun zanga-zanga, a cikin shekarar 2017.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan