Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF ta Yarjewa Enyimba taci gaba da buga wasanninta na gida tare da ‘yan kallo.
Enyimba dai sun buga wasanni a gida batare da magoya baya ba.

Domin ko wasansu da suka buga wasan zagaye na 2 tare da Rahimo F/C babu magoya baya suka buga wannan wasa wato wasan zakarun nahiyar Afrika.
Hakan dai baya rasa nasaba da rashin da’a da magoya baya suke nunawa suke jawowa a hanasu shiga su kalli wasa.

A wasan da kungiyar kwallon kafan ta Enyimba zata kara da Al-Hilal ta kasar Sudan CAF din ta yarje magoya baya sushiga su kalla.
Turawa Abokai