Iyaye Su Dinga Sanya Ido Akan Yadda Ƴaƴansu Ke Amfani Da Kafafen Sada Zumunta – Sarkin Bichi

101

Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Bayero ya yi kira da a dinga amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ya kamata domin samun cigaba mai amfani.


Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke karɓar babban sakataren hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Alhaji Ismail Na’abba a fadarsa da ke bichi.


“Muna kira ga mutane da su dinga amfani da kafafen sada zumunta yadda ya dace, domin hakan ne zai tabbatar da tarbiyyar matasanmu”


“Muna kira ga iyaye a jihar Kano da su zama masu sanya idanu akan yadda ƴaƴansu su ke amfani da wannan kafa ta sada zumunta”


Sarkin na Bichi ya buƙaci da masu shirya sana’ar finafinai da su cigaba bunƙasa al’adun Hausawa ta hanyar shirin finafinai da su ke yi. Ya ƙara da cewa akwai buƙatar wayar da kan al’umma ta hanyar amfani wasannin kwaikwayo wanda hakan zai kai ga fahimtar matsalolin da su ke cikin al’ummar Hausawa.


A nasa ɓangaren babban sakataren hukumar tace finafinai ta jiha Alhaji Ismail Na’abba, ya ce sun zo fadar ne domin neman haɗin kan masarautar domin samar da tarbiyya a cikin al’umma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan