Katsina United Sun Dauki Sabon Mai Horaswa

180

Hukumar gudanarwa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ta nada Henry Makinwa a matsayin sabon mai horas da kungiyar.

Anyi wannan nadin sabon mai horaswa karkashin jagorancin sabon shugaban kungiyar ta Katsina United wato Prince Abdussamad Badamasi.

Henry dai tsohon mai horas da kungiyoyin kwallon kafan A.B.S da Abia Warriors ne kafin komawarsa kasar wake don ci gaba da ayyukansa, inda ya rattaba kwantaragin shekara 1 a kungiyar ta Katsina United.

A ranar Litinin wannan mai horaswa zai fara aikinsa da safe inda kungiyar kwallon kafan ta Katsina United zata fafata wasannin sada zumunta da wasu kungiyoyin Kwallon Kafan a jahar ta Katsina kafin kungiyar ‘The Changi Boys’ ta fara buga wasannin share fage na sabuwar kakar wasannin ajin Premier ta kasarnan daza a fara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan