Yadda Aka Gudanar Da Taron Rufe Daurar Haddar Hadisai A Qadi Ahmad Islamiyya

140

A ranar Juma’a ne aka gudanar da ƙwarya-ƙwaryar Taron Rufe Daurar Haddar Hadisai Irinta ta Farko a Qadi Ahmad Islamiyya dake Rimin Gata a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.

Tun da farko da yake jawabi, Shugaban Tsarin Daurar Haddar Hadisan, Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, ya ce an shirya Daurar Haddar Hadisan ne bisa shawarar shugabanni, ganin cewa tuni dama ana shirya Daurar Haddar Alƙur’ani.

Ya ce an shirya ɗalibai za su haddace hadisai 200 ne a cikin kwanaki 20, amma sai aka rage suka dawo hadisai 100, saboda ƙarancin ɗalibai da kuma ƙorafin da suka yi cewa hadisan sun yi yawa.

Ya bayyana jin daɗinsa bisa yadda ɗalibai suka jajirce yayin gudanar da Daurar, ya kuma gode wa Daraktan Makarantar bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban ilimin addinin Musulunci.

Taron ya samu sa albarka daga Daraktan Makarantar, Imam Ahmad Zubair, Barrista Salisu Ado da Limamin Sabon Garin Gadan, Malam Sani Umar Ɗandago.

Dukkaninsu sun taya ɗaliban murna bisa halartar wannan Daura, sun kuma yi kira a gare su da su yi amfani da abinda suka koya.

Daga ƙarshe an bada Takardun Shaidar Halarta ga ɗalibai 11 da suka halarci Daurar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan