Zakaran nan mai suna Maurice ya yi nasarar a Kotu bayan an gwabza a kotu kan karar da aka shigar na uwar dakinsa sakamakon yadda ya ke damun makwafta da cara, indakotu ta ce ai shi ma zakaran na da damar yin cara da tsakar rana.
Wannan kara da makwafatan uwar dakin Maurice, mai suna Corinne Fesseau suka shigar ta shahara a kafafafen yada labarai a sassan duniya, inda ake ganin cewa alamu ne na irin zaman tankiya da ke tsakanin mai zakara da makwaftan ta.
Lauyan Fesseau, uwar dakin zakara Maurice, Julien Papineau ta ce zakara ya yi nasara a kotu, kuma za a biya shi diyyar kudi har Yuro dubu 1, kwatankwacin naira dubu 400.
Fesseau ta shaida wa kotu cewa babu wandaya taba yin korafi game da carar da zakaran ta Maurice ke yi, bayan da wasu ‘yan fansho suka suka sayi wani gida kusa da ita.
Jean – Louis wanda tsohon manomi ne damatars Joelle daga yankin Haute – Vienne a tsakiyar Faransa sun yi ikirarin cewa tun wajen karfe 4 na asuba Maurice ke damun su da cara.
Fesseau ta ce ta yi iya kokarin tadon gani zakaranta Maurice ya yi tsit amma abin ya ci tura.
Bayan hukuncin, a wajen kotun, Fesseau ta saka cara irin ta zakara don nuna farin cikin ta inda ta ke cewa ba ta san mai za ta ce ba, tana mai cewa ‘wannan nasara ce ga duk wanda ya ke cikin irin yanayin da na ke ciki’.
[…] Muƙalar Da Ta GabataZakara Ya Yi Nasara A Kotu […]