An Kammala Jigilar Alhazan Kano

254

A ranar Lahadin nan ne rukunin ƙarshe na alhazan Jihar Kano na bana suka sauka a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano.

Majiyarmu ta ruwaito cewa alhazan waɗanda adadinsu ya kai 160 sun bar Filin Jirgin Saman Sarki Abdul’aziz dake Jidda da misalin ƙarfe 1:40 na rana.

Jirgin da ya ɗauko alhazan ya sauka a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasar na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 5:45 na yamma.

Jaridar KANO TODAY ta ruwaito cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta yi jigilar alhazan Kano kimanin 3,170 ne zuwa Saudiyya don sauke farali a bana.

Babban Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Danbatta ya yabi alhazan na Kano bisa yadda suka nuna kyawawan halaye.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan