Ban Tsani Musulunci Ba- Wike

84

Kimanin makonni biyu da yi masa zargin rushe masallaci, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa shi bai tsani Musulunci ba ko wani addini.

A ranar Lahadi ne Gwamna Wike ya yi wannan tsokaci lokacin da yake nuna wa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi filin da ake zargin ya rushe masallacin a Fatakwal.

Wata sanarwa da Shugaban Sashin Watsa Labarai da Huɗɗa da Jama’a na NGF, Abdulrazaque Bello Barkindo ya fitar a Abuja, ta ce Gwamna Fayemi ya je Fatakwal ne don tabbatar da gaskiyar lamari game da rushe masallacin.

Gwamna Wike ya yi iƙirarin cewa babu wani masallaci a wurin, saidai wata hanyar ruwa.

“Ban tsani Musulunci ba ko wani addini.

“Kamar yadda za ku iya gani, ba a taɓa gina wani masallaci a wajen nan ba, wata hanyar ruwa ce wadda ake ta ce-ce-ku-ce a kanta tsakanin Gwamnatin Jihar da wasu ƙungiyoyi saboda suna so su yi gini a haramtaccen fili”, in ji Gwamnan.

Gwamna Wike ya nuna jin daɗi bisa yadda Shugaban na NGF, wanda ya samu rakiyar Darakta Janar na Ƙungiyar, Asishana Okauru ya samu lokaci na ziyartar jihar don tabbatar da gaskiyar lamari.

Ya kuma yabi tsarin shugabanci na Gwamna Fayemi, wanda ya bayyana a matsayin abin koyi, yana mai lura da cewa bai bi sahun waɗanda suke gaggawa wajen yanke hukunci game da al’amarin ba.

A cewar sanarwar ta NGF, “waɗanda ke yamaɗiɗin rushe masallacin masu shirya makirci ne”.

“Babu wani abu da zai nuna an taɓa gina masallaci a wajen”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan