Beraye Sun Zama Annoba A Ƙasar Amurka

256

An bayyana cewar za’a fara amfani da wani tarko wanda za’a dinga saka barasa domin yaki da ɓeraye a garin Brooklyn dake gundumar birnin New York birni mafi girma a Amurka.


Magajin garin Brooklyn Eric Adams, ne ya gabatar da wannan sabon tarko mai suna “Ekomille” ga manema labarai.


Eric Adams ya ƙara da cewa tarkon zai janyo ɓaraye saboda abincin da aka sanya a samansa wanda da zarar sun hau zasu fada cikin bokiti mai cike da ruwan barasa.


Shugaban kamfanin Rat Trap Inc. da ya kirkiro tarkon Anthony Giaquinto ya bayyna cewar an yi amfani da wani nau’in giya da zata sanya byerayen buguwa daga bisani kuma su nutse a ciki.


Tun da farko wannnan tarkon zai iya kashe beraye 80 a rana. Ana dai yawan yin korafe-korafe akan beraye a birnin abinda ya zama tamkar annoba.


A binciken da jami’ar Columbia ta kudanar a shekarar 2014 ya nuna cewa akwai beraye fiye da miliyan biyu a garin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan