Tsananin Zafi Ya Kashe Mutane Dubu 1 Da 500 A Ƙasar Faransa

125

Gwamnatin ƙasar Faransa ta bayyana cewa, sama da mutane dubu 1 da 500 ne suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in tsananin zafi da ya afka wa kasar a kwanakin baya.


Ministar Lafiyar ƙasar ta Faransa, Agnes Buzyn ta ce, sun tattara alkaluman mutane dubu 1 da 500 da suka mutu a cikin watanni biyu, amma ko kusa wadannan alkaluma basu kai wadanda aka samu a shekarar 2003 ba, lokacin da makamancin wannan ibtila’in ya lakume rayuka dubu 15.


Tsananin zafin na shekarar bana, ya afka wa Faransa ne a cikin watannin Yuni da Yuli, inda ya kai digiri 46 a ma’aunin Celsius musamman a yankin kudancin ƙasar.


A shekarar 2003, tsananin zafin ya addabi jama’a ne cikin kwanaki 20 na watan Agusta, yayin da a bana, ya shafe kwanaki 18 yana hana mutane sukuni a mabanbantan lokuta biyu.


Ministar Lafiyar ta ce, matakan kariyar da hukumomin kasar suka dauka, sun taimaka wajen rage alkaluman mace-macen a bana, idan aka kwatanta da shekarar 2003.


Tarihi ya nuna cewa, shekarar ta 2003, ita ce wadda aka fi samun asarar rayuka sakamakon tsananin zafin a Faransa, inda a wancan lokacin ibtila’in ya fi kamari a birnin Paris da yankin tsakiyar kasar.

Rahoton Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan