Ofishin Jakadancin Najeriya dake Afirka ta Kudu ya ce a ƙalla ‘yan Najeriya 400 ne suka nuna sha’awa da kuma yin rijistar dawowa gida biyo bayan hare-haren ƙin jinin baƙi da ‘yan Afirka ta Kudun ke ci gaba da kaiwa.
Ƙaramin Jakadan Najeriya dake Johannesburg a Afirka ta Kudu, Godwin Adama ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Abuja ranar Lahadi.
Mista Adama ya ce Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen Sama na Air Peace ya yi tayin dawo da ‘yan Najeriya dake muradin dawo gida kyauta biyo bayan hare-haren ƙin jinin baƙi da ‘yan Afirka ta Kudu ke kai wa ‘yan Najeriya da wuraren kasuwancinsu.
A ta bakinsa, a ranar Larabar wannan makon ne za a dawo da rukunin farko na ‘yan Najeriya dake da muradin dawowa gida.
“Wannan jirgi zai ishe mu. Fiye da ‘yan Najeriya 400 ne suka yi rijista, waɗansu da yawa na ci gaba da zuwa”, in ji shi.
Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Kabiru Bala, ya ce ‘yan Najeriya sun nuna sha’awarsu ta dawowa gida cikin ɗabi’a mai kyau.
Bala ya ce: “Muna tattara bayanansu. Waɗanda ba su da takardun tafiya, za mu samar musu ta takardun tafiya na gaggawa.
“Akwai sauran ƙa’idojin da gwamnati ta sa waɗanda dole mu bi. Dole a sanar da hukumomin da suka dace a Najeriya, kuma dole su zama cikin shirin karɓar waɗanda za su dawo ɗin.
“Ana ci gaba da aiki tuƙuru a Babban Ofishin Jakadanci da Ƙaramin Ofishin Jakadanci bisa wannan batu. Da zarar an kammala bin ƙa’idoji da dokokin da suka wajaba, za a fara dawo da su babu shakka.
“Ana buƙatar a ƙara haƙuri kaɗan, hakan zai taimaka. Yadda ‘yan Najeriya suka nuna halayya abu ne mai ƙayatarwa.
Haka kuma, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Najeriya dake Afirka ta Kudu, Ben Okoli, ya ce suna ci gaba da ƙoƙari don ganin an fara kwaso ‘yan Najeriya dake buƙatar dawowa gida.
“Ƙaramin Ofishin Jakadancin yana warware batun takardun tafiya. Ana ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya rijista, kuma ana ba su takardun tafiya da suka zama wajibi don ba su damar dawowa ta Legas.
“Wasu sun rasa fasfo-fasfo ɗinsu a gidajensu da wuraren kasuwancinsu saboda gobara ta laƙume su, yayinda wasu kuma aka an sace musu takardun tafiya da kuma dukiyoyinsu”, in ji Mista Okoli.
Ya ce Ƙungiyar na ci gaba da matsa lamba wajen ganin cewa an biya ‘yan Najeriya diyya saboda suna da isasshiyar hujja dake nuna cewa waɗannan hare-hare an tsara su ne kuma da gayya ake kai su.
[…] Muƙalar Da Ta GabataXenophobia: Gwamnatin Tarayya Ta Sa Ranar Da Za Ta Fara Dawo Da ‘Yan Najeriya Gida […]