Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje a ƙalla sau 52 tun lokacin da aka rantsar da shi a wa’adin mulkinsa na farko a watan Mayun 2015 zuwa yanzu, inda ya kashe a ƙalla Naira Biliyan 4, kamar yadda binciken jaridar The Daily Times ya nuna.
Bincike ya nuna cewa kawo yanzu Shugaba Buhari ya ziyarci ƙasashe 30 dake a nahiyoyi huɗu, da suka haɗa da Afirka.
A cewar binciken da The Daily Times ta yi, kawo yanzu, Shugaba Buhari ya ziyarci ƙasashen Afirka 16, ƙasashen Asiya bakwai, ƙasashen Turai biyar, sai ƙasa ɗaya a Amurka ta Yamma.
A cikin ƙasashe 30 da Shugaban ya ziyarta, ƙarin bincike ya nuna cewa ya ziyarci Amurka da Birtaniya sau biyar kowace, sai Faransa, Cadi da Saudiyya da ya ziyarta sau uku kowace.
Ƙasashen da ya ziyarta sau biyu sun haɗa da Nijar, China, Jamus, Afirka ta Kudu, Benin, Gana, Haɗaɗdiyar Daular Larabawa, Kenya, Senegal da Gambiya.
Ƙasashen da Shugaba Buhari ya ziyarta sau ɗaya sun haɗa da Kamaru, Indiya, Sudan, Iran, Malta, Ethiopia, Ƙatar, Equatorial Guinea, Moroko, Mali, Poland, Jodan, Laberiya da Japan.
Haka kuma, binciken da aka yi game da tafiye-tafiyen Shugaban na cikin gida ya nuna cewa akwai jihohin da har yanzu bai ziyarta ba idan ba da dalilin kamfen ko zaɓe ba.
Binciken na The Daily Times ya nuna cewa Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma su ne kaɗai yankunan da Shugaba Buhari ya ziyarci kowace jiha, inda mahaifarsa ta Katsina ta samu ziyara mafi yawa.
Ziyararsa zuwa Jihohin Anambra, Ondo, Kogi, Bayelsa da Akwa Ibom duk ziyarce-ziyarce ne na kamfen ga jam’iyyarsa ko dai a zaɓen shugaban ƙasa ko na gwamna.
Sauran sun haɗa da Jihohin Delta, Ekiti, Oyo da Abia.
Ƙarin bincike ya nuna cewa yayinda Shugaba Buhari ya ziyarci ƙasashe 30 a shekaru huɗu da wata uku, tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya ziyarci a ƙalla ƙasashe 30 daga 2010 zuwa 2015, yayinda tsohon Shugaban Ƙasa, Olesegun Obasanjo yake da tarihin ziyartar ƙasashe 97 daga 1999 zuwa 2007.
Idan dai za a iya tunawa, tsaffin Shuwagabannin Ƙasa, Jonathan da Obasanjo sun sha suka bisa tafiye-tafiyensu zuwa ƙasashen waje lokacin da suke kan karagar mulki.
Bayan da tsohon Shugaba Jonathan ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje a ƙalla sau 20 a 2012, ‘yan adawa sun kamanta tafiyarsa da ta Obasanjo, wanda a wani lokaci a baya, mutane da dama suka bayyana shi a matsayin Shugaban Ƙasar da ya fi kowa yin tafiye-tafiye, wanda ke da tarihin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare sau 93 a shekaru uku na farko a karagar mulki.
A cewar rahotonni, ya shafe a ƙalla kwanaki 340 a wajen ƙasar nan a lokacin shugabancinsa, ya yi tafiya sau 400 daga 1999 zuwa 2007.
Obasanjo, kamar Buhari, da yake gabatar da jawabi a Jami’ar Oxford ya ce tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare da yake yawan yi na da manufar dawo da martabar ƙasar nan da ta riga ta zube a idanun ƙasashe biyo bayan shekarun da sojoji suka yi suna mulki.
Obasanjo ya ce: “An zaɓe ni a matsayin Shugaban Najeriya a watan Fabrairu na shekarar 1999, an kuma rantsar da ni a matsayin Shugaban Ƙasa a watan Mayu, 1999, lokacin da Najeriya take wata ƙasa da ake ƙyama.
“A ko’ina mutane suna da ra’ayi mara kyau game da mu. Ana gudun mu ɗin mu da ganin mu a matsayin wani nauyi a cikin ƙasashe.
“Yanayin yana buƙatar in yi aiki don in warware waccan fahimtar. A matsayin ƙasa ƙarƙashin sauyin siyasa, na miƙa kaina gaba ɗaya don fuskantar aikin da yake gabana.
“A shekaru takwas da na yi ina mulki, na je wajen shugabannin ƙasashe, zan kuma ci gaba da yin haka har bayan shuagancina. Wannan shi ake kira ‘shuttle diplomacy’ a shugabanci.
“Na yi tafiye-tafiye sosai, ina nemo fahimtar ƙasashe, da kuma shigarmu zuwa sabuwar duniya ‘yar yayi, ba ga Najeriya kaɗai ba, amma ga dukkan nahiyar Afirka. Zuwa lokacin da na gama wa’adin mulkina na biyu, na yi tafiya zuwa ƙasashe 97”.
Yayinda haka ke faruwa, jam’iyyar PDP ta soki Shugaban da yunƙurin zagaye ƙasashen duniya duk da taɓarbarewar tattalin arziƙi da tsaro a ƙasar nan.
Jam’iyyar ta ce abin kaico ne maimakon tafiye-tafiyen Buhari su zama masu inganta tattalin arziƙi, mafi yawansu sun zama tafiye-tafiye na shaƙatawa.
Sakataren Watsa Labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya faɗa wa The Daily Times cewa a baya PDP ta riga tuhumar Shugaban bisa tafiye-tafiyensa na alamunbazaranci, waɗanda suka sa ƙasar nan asarar biliyoyin Naira.
Mista Ologbondiyan ya ce waɗannan fa banda kuɗaɗen masu biyan haraji ne da ake kashewa ga tafiyar Buhari ta neman lafiya a Birtaniya, yana mai ƙaryata iƙirarin da na hannun damar Buhari ke cewa tafiye-tafiyensa suna amfanar ƙasar nan ta ɓangaren tattalin arziƙi.
Maimakon haka, jam’iyyar ta ce tafiye-tafiyensa ba su samar wa ƙasar nan ƙaruwar zuba jari daga ƙasashen waje ba, saidai rasa sana’o’i da ayyuka.
Amma, da dogarai da abokan Shugaba Buhari ke bada kariya, sun ce Najeriya ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC ta amfana da tafiye-tafiyen da ya yi tunda ya hau kan karagar mulki.
An jiyo Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu, yana mayar da martani ga masu sukar yawan tafiye-tafiye na Shugaban, yana mai bada kariya ga buƙatar yin tafiye-tafiyen, yana mai cewa ‘Waɗannan tafiye-tafiyen da Shugaban ke yi ba na shan shayi ba ne, sai don amfanin ƙasar nan”.
Ya ƙara da cewa Shugaban ya yi tafiye-tafiye don tattaunawa da shugabannin ƙasashen duniya bisa yadda za a dawo wa Najeriya kuɗaɗe da aka sace aka jibge a asusun bankuna na ƙasashen ƙetare, don ya nemi taimako daga shugabannin ƙasashe bisa shirinsa na yaƙi da cin hanci, haɓaka kasuwanci da zuba jari da kuma raya abubuwan more rayuwa na ƙasar nan da suka taɓarɓare kamar layin dogo, wutar lantarki da hanyoyi da sauran muhimman ɓangarori.
Shi ma, Shugaban Ƙungiyar Watsa Labarai ta Buhari, Niyi Akinsuji, ya dira a kan masu sukar Buhari, musamman jam’iyyar hamayya ta PDP, bisa sukar tafiye-tafiyen Shugaban zuwa ƙasashen ƙetare.
Ya yi zargin cewa a kodayaushe PDP takan shiga cikin ce-ce-ku-ce da ba buƙatar shigar su, yana mai cewa kowane ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen Shugaban tana da dalili ta kuma haifa wa ƙasar nan ɗa mai ido.