Home / Siyasa / Da ɗumi-ɗumi- Kotu Ta Soke Zaɓen Wani Ɗan Majalisar Wakilai na APC A Kano

Da ɗumi-ɗumi- Kotu Ta Soke Zaɓen Wani Ɗan Majalisar Wakilai na APC A Kano

Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe ta Kano ta soke zaɓen Munir Dan’Agundi, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kumbotso a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.

Umar Balla na jam’iyyar PDP ne ya shigar da ƙarar, inda yake ƙalubalantar zaɓen Mista Dan’Agundi, wanda ya ce ya gaza samun mafi rinjayen sahihan ƙuri’u da aka kaɗa.

Da take yanke hukunci ranar Talatar nan, Kotun ta soke zaɓen Mista Dan’Agundi, ta kuma bada umarnin a sake sabon zaɓe a Tashar Zaɓe ta Tsamiya, a Mazaɓar Mariri.

About Hassan Hamza

Check Also

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *