Flying Eagles Zasubuga Wasan Zagaye na Biyu Da Sudan

159

Kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 23 wato Flying Eagles zasu kara wasan zagaye na biyu da kasar Sudan a yau Talata.

Wasan dai na zagaye na biyun wasan share fage ne na neman tikitin buga gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Inda a wasan farko da aka fafata a can kasar ta Sudan Najeriya sunyi rashin nasara daci 1 da nema.

A yau Najeriya na bukatar ta jefa kwallaye guda biyu da nema domin samun damar shiga gasar, idan kuwa har suka gaza yin nasara to babu makawa bazasu sami tikitin buga gasar ba.

Wasan dai za a fara yinsa da misalin karfe 4:00 agogon Najeriya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan